Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu ba ta sauya matsayarta ba game da cire tallafin man fetur, kamar yadda shugaban ƙasar ya sanar a ranar 29 ga watan Mayu, 2023. A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Bayo Onanuga, ta bayyana cewa: “Gwamnati na son jaddada cewa matsayarta kan cire tallafin man fetur ba ta sauya ba daga abin da shugaba Bola Tinubu ya bayyana a ranar 29 ga watan Mayu, 2023” “Zamanin tallafin man fetur ya ƙare. “Ba a ware naira tiriliyan 5.4 kan tallafin man fetur ba a kasafin kuɗin 2024, kamar yadda ake ta raɗe-raɗi a kai”.

Tun farko dai bayanai sun nuna cewa akwai yiwuwar Najeriya ta kashe kuɗi har naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024 kan tallafin man fetur, wanda hakan ya nunka abin da ƙasar ta kashe a 2023 kan tallafin na man fetur. Sannan gwamnatin Najeriyar za ta ranto ƙarin kuɗi naira tiriliyan 6.6 domin cike giɓin kasafin kuɗin ƙasar – in ji kamfani dillancin labaru na Reuters. Shawarwarin da aka miƙa wa shugaban ƙasar kan tsarin daidaitawa da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa wanda aka yi wa take ‘Accelerated Stabilisation and Advancement Plan’ a turance – wanda ma’aikatar kuɗi tare da ɓangaren ƴan kasuwa suka rubuta, na da manufar magance ƙalubalen da suka shafi sauye-sauyen da gwamnati ta kawo domin bunƙasa ci gaban ƙasa. A watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya soke tallafin man fetur, wani mataki da masu zuba jari suka jinjina mawa. Sai dai hakan ya jefa al’ummar ƙasar cikin mawuyacin hali, inda farashin sufuri da na kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi.

<\p>

News

Comments

Popular posts from this blog

News English to Hausa