Hello, World! From jafaru ibrahim Anguwa iya jaji

BARKA DA ZUWA WANNAN CHANEL

Lokacin da maharan suka shigo garinmu, na ji ƙarar harbe-harbe, sai na yi sauri na hau kan babur ɗina na tsere a cikin duhun dare, na bar matata da ƴaƴana da tsofaffin iyayena," kamar yadda wani mazaunin garin Kuchi ya shaida wa BBC, (ba za mu ambaci sunansa ba saboda dalilai na tsaro) Mazaunin garin ya ce ya zaɓi ya ceci ransa tukuna inda ya tsere zuwa Minna, babban birnin jihar Neja ta tsakiyar Najeriya. Amma kuma ya damu matuƙa da halin da iyalansa ke ciki. “Mahara sun kama matata da kuma yayarta. Amma daga baya matata ta tsere musu a lokacin da masu garkuwan ke ƙoƙarin kai su wurin da za su tsallaka kogin Shiroro.” in ji mazaunin garin. Sai dai har yanzu masu garkuwan suna tsare da ƴar'uwar matarsa yayin da masu garkuwan sun riga sun kira ƴan'uwan waɗanda aka sace domin neman kuɗin fansa.

Comments

Popular posts from this blog

News English to Hausa