Daji mafi girma

photos

09033343991 wanna lambar jafaruibrahim

Masana kimiyya sun gano wani wuri da suka yi amannar shi ne daji mafi daɗewa a duniya, mai ɗauke da wasu bishiyoyi a kudu Maso Yammacin Ingila. An gano shi ne a saman wani tsauni kusa da Minehead, Somerset da ke kusa da wani sansannin Butlin da ake zuwa hutu. Masu bincike daga jami'ar Cambridge da Cardiff sun ce bishiyoyin da aka gano su ne mafi daɗewa a Burtaniya kuma su aka sani mafi daɗewa a yanzu a duniya. An fi sanin bishiyoyin da Calamophyton tana kama da bishiyar kwakwar manja. An kwatanta ta da bishiya mafi tsayi a duniyarmu ta yau, inda ta kai tsayin mita biyu zuwa hudu. Kazalika sun bayyana bishiyoyin da tsayin jijiyoyi da kuma tsari na daban. Sun fito da bayanan yadda bishiyoyin suka taimaka wajen riƙe kasa, suka kuma fitar da zanen gaɓar tekun na tsayin daruruwan shekaru da suka gabata. "Lokacin da na fara ganin hoton bishiyoyin nan da nan na gano yadda suke, saboda kwashe shekara 30 da na yi ina karantar irin waɗannan bishiyoyin a faɗin duniya," in ji Dr Christopher Berry na makarantar nazarin ƙasa da kimiyyar muhalli a Cardiff. "Abin birgewa ne ganin irin waɗannan bishiyoyin a kusa da gida. Amma abin ba da labarin shi ne yadda ake kallon su idan an ɗaga kai sama, kuma sun girma a wuri mai kyau."

Comments

Popular posts from this blog

News English to Hausa