Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu ba ta sauya matsayarta ba game da cire tallafin man fetur, kamar yadda shugaban ƙasar ya sanar a ranar 29 ga watan Mayu, 2023. A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Bayo Onanuga, ta bayyana cewa: “Gwamnati na son jaddada cewa matsayarta kan cire tallafin man fetur ba ta sauya ba daga abin da shugaba Bola Tinubu ya bayyana a ranar 29 ga watan Mayu, 2023” “Zamanin tallafin man fetur ya ƙare. “Ba a ware naira tiriliyan 5.4 kan tallafin man fetur ba a kasafin kuɗin 2024, kamar yadda ake ta raɗe-raɗi a kai”. Tun farko dai bayanai sun nuna cewa akwai yiwuwar Najeriya ta kashe kuɗi har naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024 kan tallafin man fetur, wanda hakan ya nunka abin da ƙasar ta kashe a 2023 kan tallafin na man fetur. Sannan gwamnatin Najeriyar za ta ranto ƙarin kuɗi naira tiriliyan 6.6 domin cike giɓin kasafin kuɗin ƙasar – in ji kamfani dillancin labaru na Reuters. Shawarwarin da ...